Sarkin Kano ya yi kira ga al'ummar Kano - SAHEL ENTERTAINMENT

Follow us on Facebook

ads

Hot

Post Top Ad

Friday, March 15, 2019

Sarkin Kano ya yi kira ga al'ummar Kano

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll ya yi kira ga al'ummar Kano da su zauna
lafiya kuma su kwantar da hankali da kuma kiyaya yada jita jita.
Wannan kiran na zuwa ne bayan da aka gudanar da zaben gwamnoni da kuma 'yan
majalisar jiha a fadin kasar a ranar 9 ga watan Maris.
Sarkin ya bayyana cewa hukumar INEC ce kadai ke da 'yancin bayyana sahihin
sakamakon zabe, inda hukumar ta bayyana cewa zaben bai kammala ba, kuma
akwai wasu mazabu da za a sake zabe a jihar. Daga nan, sarkin ya yi godiya ga kwamishinan 'yan sandan jihar CP Mohammed Wakili da sauran jami'an tsaro musamman kan irin rawar da suka taka wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.
Tun bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da cewa zaben jihar bai kammala ba,
ake samun fargaba a jihar.
Jigga-jigan manyan jam'iyyun jihar Kano, Ganduje da Kwankwaso sun nemi
jama'ar jihar da su zauna lafiya.
Hakan na zuwa ne a ci gaba da zaman dar-dar da ake yi a cikin jihar lokacin ake
jiran sakamakon zaben a ranar Litinin.
A ranar Lahadi ne wasu magoya bayan wasu 'yan takara suka fara murnar lashe
zaben, wanda hakan ya sanya rundunar 'yan sandan jihar ta yi gargadi da a
daina, kuma a jira hukumjar zabe ta bayyana sakamako.
Babban jami'in tattara sakamako zabe a Kano Farfesa B.B Shehu ne ya sanar da
cewa ba a kammala zabe a Kano ba, a ranar Litinin.
Ya ce Abba Kabir Yusuf na babbar jam'iyyar hamayya PDP ya samu kuri'a 1,014,474
yayin da gwamna mai ci na jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri'a
987,819.
Jam'iyyar PRP ce ta zo a matsayi na uku da kuri'a 104,009.
An ki bayyana wanda ya lashe zaben ne saboda bambancin kuri'un da ke tsakanin
manyan 'yan takarar ba shi da yawa.
Abin da ya sa dole a sake zabe a wasu mazabu da tun da farko aka soke su.
Hukumar INEC dai ba ta bayyana ranar da za ta sake gudanar da zabukan ba
tukuna.

Source: https://www.bbc.com/hausa/labarai-47542283

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad