Dan takarar gwamnan jihar Yobe kuma sakataren jam’iyyar APC na kasa, Alhaji Mai Mala Buni ya karyata jita-jitar da ake ta yadawa a wasu kakafun sadarwa na bogi cewa zai auri fitacciyar jarumar finafinan Hausa, wato Jamila Nagudu.
Mai Mala Buni ya ce labarin ba shi da madogara bare tushe, kawai yarfe ne irin na masu adawar siyasa.
A yayin tattaunawarsa da jaridar RARIYA, sakataren na APC ya bayyana cewa hoton sa da aka dinga yadawa da jaruma Jamila Nagudu ba wai shi da ita kadai bane suka dauka, sun dauka ne da sauran abokan sana’arta a yayin ziyarar da suka kawo masa a matsayin sa na jigo a jam’iyyar APC. Amma sai aka yanke aka bar iya shi da ita don kawai biyan bukatar masu adawa.
“Kowa ya san yadda gwamnatinmu ta APC take da alaka da ‘yan fim din Hausa da na Turancin da kuma mawaka. Kuma sun bada gudummawa matuka a nasarar da APC ta yi a zaben 2015. Wanda hakan ya kara dankon zumunci tsakanin su da shugaba Buhari da sauran jiga-jigan APC”, cewar Mai Mala Buni.
Mala Buni ya kara da cewa yana daga cikin irin gudummawar da mawaka da ‘yan fim suka bayar a wannan gwamnati, irin wakoki da finafinan da suka yi a kan gwamnatin Buhari. Don haka akwai kyakkyawar alaka taakanin su da ‘yan fim a siyasance.
Sannan kuma irin ziyarar da ‘yan fim din suka kai masa sun kai shugaba Buhari irin ta a Villa ba sau daya ba sau biyu ba.
An zargi wani hadimin dan takarar gwamnan jihar Yobe a PDP, mai suna Najib da yada farfagandar auren, wanda kuma wannan ba shine karo na farko ba da yake yada farfaganda a kan jiga-jigan APC na jihar Yobe.
“Jam’iyyar APC ta jama’a ce musamman talakawa da matasa wanda hakan ya sa a koda yaushe matasa suke yawan ziyartar wasu jiga-jigan APC domin nuna goyon bayan su ga gwamnatin Buhari.
No comments:
Post a Comment