Jita-jitan mutuwar Aliyu ya mamaye ko ta ina a yanar gizo duka, amma abin mamaki Aliyu Mohammed Sani ya fito ya bayyana da cewa bai mutu ba. kamar yadda gidan jaridan Daily Trust ke bada tabbacin haka.
“Alkawari ne nayi da cewa idan har shugaba Muhammadu Buhari ya lashe tseren takaran kujerar shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu ga zaben 2019, zan yi wanka da ruwar kwata, zan kuma sha kwata”
“Na kuma cika alkawari na. A yayin da aka gabatar da Buhari a matsayin mai nasara ga zaben, na shiga kwata kamar yadda na yi alkawari, na kuma sha ruwar kwatan a gaban jama’a. Duk wata zancen cewa na mutu sakamakon aman jini ko wata ciwon ciki, ba gaskiya bane. Ina lafiya lau, kuma ina garau” Inji Aliyu.
Sahel Entertainment ta gano cewa Aliyu na da aikin hannun sa na fenti.
“A yadda ni ke gabatar da wannan bayanin, ina shirye kan komawa Bauchi daga wata aikin fenti da ya kawo ni inda nake yanzun nan” inji shi.
Karanta Labarin:N-power 2019
No comments:
Post a Comment