Gwamnatin tarayya ta samu labarin cewa mutane da dama ana rudan su da cewa fom na N-Power ta shekarar 2019 ya fito. Harma wasu sun bayar da kudin su a layin yanar gizon ga mutanen da basu sani ba, wai don su taimaka masu da cika fom din. Bisa ga wannan dalilin ne ita gwamnatin tayi kira ga mutane da su lura sosai wajen yin mu'amala da 'yan damfara mussamman ta hanyar yanar gizo. da kuma gujewa duk wani labari da yazo musu game da N-power idan ba ta hanyar sadarwarsu ta Twitter, facebook da sauransu ba. Kana da haka gwamnatin ta kara da cewa fom din na daf da fitowa. saboda haka mutane su kara da hakuri
Sahel Entertainment tayiyi alkawarin sanar da ku a duk lokacin da aka fara cikawa tare da matakai da zakabi domin cika fam din idan lokaci ya gabato. Mun bukaci ka bi wannan shafi na mu; Sahel Entertainment a kowace lokaci. A nan ne zamu sanar maku da cikakken labari da kuma matakan da za a dauka har ka kai ga cika fom din ba tare da samun wata matsala ba.
Mista Afolabi Imoukhuede, Babban shugaba mai taimakawa ga shugaba Muhammadu Buhari wajen samar da ayuka a kasa, ya bayyana a shafin yanar gizon nishadarwa ta Facebookr da cewa lallai gwamnatin tarayya bata bude layin cika fom na N-Power ba tukun na, amma za a yi hakan idan an kamala zaben tarayya ta Najeriya gaba daya.
“Gwamnatin tarayya bata saki fom na N-Power ba tukun na, amma za ta yi hakan bayan an kamala hidimar zaben kasar Najeriya gaba daya” inji fadin Mista Afolabi a layin Facebook da N-Power ke amfani da ita a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2019 da ta gabata.
“Zamu kuma sanar da duk wata mataki akan hakan idan lokaci ya yi na sake cika fom din” inji shi.
Mista Afolabi ya gabatar da hakan ne a yayin da yake mayar da martani ga jita-jita da tambayoyi da mutane ke ta aikawa game da zancen fom na N-Power ta shekarar 2019.
No comments:
Post a Comment