A kalla mutum 49 ne aka kashe kuma sama da 20 suka samu raunuka masu muni bayan da aka kai hari a masallatai biyu a Christchurch da ke New Zealand. An kama mutum hudu da ake zargi suna da hannu a harin- an bayyana daya daga cikinsu dan kasar Ostireliya a matsayin mai tsattsauran ra'ayin ta'addanci. Shugabanni da mutanen duniya sun yi Allah-wadai da harin inda gwamnatin kasar ta sha alwashin hukunta maharan. Gwamnatin New Zealand ta shawarci musulmai da su kulle masallatansu har sai baba ta gani.
https://www.bbc.com/hausa/labarai-47587706
No comments:
Post a Comment